IQNA

‘Yan Ta’addan daesh Sun Kare Kansu Da Ayar Kur’ani Dangane Da Kisan Dan Jordan

16:52 - February 04, 2015
Lambar Labari: 2809490
Bangaren kasa da kasa, yan ta’addan kungiyar daesh sun kare kansu dangane da kisan da suka yi sojan sama na kasar Jordan Mu’az Kasasibah da wata daga cikin ayoyin kur’ani mai tsarki.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Manarah cewa, kungiyar ISIS ta kare kanta dangane da kisan da da ta yi wa sojan sama na kasar Jordan Mu’az Kasasibah da wata daga cikin ayoyin kur’ani mai tsarki sakamakon sukar da suke sha.
'Yan ta'addan ISIS sun fitar da wani faifan bidiyo a yammacin yau, wanda ke nuna cewa sun kashe matukin jirgin yaki dan kasar Jordan Mu'az Al-kasasibah da suke garkuwa da shi, ta hanyar kone shi da wuta kurmus.
Kungiyar ta'addanci ta Da'esh ko (IS) dake da'awar kafa daular musulinci a kasashen Iraki da Syria ta fitar da sabon faifan bidiyo wanda a cikin sa ta kona wani mutun da ran sa wanda tace shine matukin jirgin nan na kasar Jordan da take garkuwa dashi.  
A cikin faifan bidiyo wanda hankali baya dauka na mintuna ashirin da biyu an nuno wani mutun sanyeda kaya launin ruwan goro wanda kungiyar ta ce shine Maaz al-Kassasbeh dan kasar Jordan din yana konewa da ran sa cikin wani keji na karfe mai ci da wuta.  
Shi dai al-Kassasbeh shine matukin jirgin Jordan da kungiyar ta Da'esh tace ta kama kuma take garkuwa dashi yau sama da wata guda bayanda jirgin sa kirar ya rikito a wani yankin kasar Syria. 
Wadannan yan ta’adda dai suna fakewa ne da irin bayanan da suke cikin fatawoyin da wasu malamai suka yi ne da ake dauke da irin wannan akida tun a tsawon tarihi.
2807123

Abubuwan Da Ya Shafa: jordan
captcha