Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na France 24 cewa,a cikin lokutan ana kara samuun kin jinin addinin muslunci da mabiyansa na ci gaba da karuwa a kasar Sewden tun bayan abubuwan da suka faru a cikin kasashen yankin nahiyar turai inda ake kai hare-hare kan masallatai da cibiyoyin musulmi.
Bayanin ya ci gabada cewa akwai dubban mutane da suke zaune a kasar ta Sweden wadanda sun fito ne daga kasashen larabawa da na musulmi wadabnda wasunsu sun samu zama ‘yan kasar, amma kuma suna fuskantar cin mutunci da batunci daga sauran al’ummar kasar saboda su musulmi ne, wanda kuma hakan yay i hannun riga da dukkanin dokokin da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar.
Dangan eda wanann batu kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar duniya ya fitar da bayani da a ckinsa yake nuna damuwa dangane da irin halin da musulmi suke ciki a kasar Sewden tun bayan faruruwa ayyukan ta’addancia cikin wasu kasashen turai.
Yanzu haka dai musulmin na Sweden an cikin damuwa da fargaba, ganin cewaa kone lokaci ba su cikin aminci, kuma ana kai musu hari a kan masallatansu da cibiyoyinsu na addini tare da ke alfarmarus da iyalansu.
2808253