IQNA

Dubban Mutane Sun Nuan Fushinsu Sakamakon Kone Kur’ani A Garin Jalo Na Libya

23:13 - February 10, 2015
Lambar Labari: 2834848
Bangaren kasa da kasa, dubban mutane ne suka fitoa cikin fushi domin nuna rashin amincewarsu da kone ayoyin kur’ani mai tsarki da wasu mutane da ba a sani ba suka yi a masallacin Zawiyatol Irq da ke garin jalo a gabacin Libya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Akhbar Libya 24 cewa, cincirindon mutane sun fitoa  cikin fushi domin nuna rashin amincewarsu da kone ayoyin kur’ani mai tsarki da wasu mutane ba suka yi a masallacin Zawiyatol Irq da ke garin jalo a gabacin Libya wadanda ba a san ko su wane ne ba.
Bayanin ya ci gaba da cewa wasu wasanda suka ganewa idanunsu abin da ya faru sun tabbatar da cewa wadanda suka yi wanann lamari sun tsere ba tare da an kame sub a, lamarin da ya harzuka jama’a suka yi ta fitowa daga kowane bangare na garin Jalo domin la’anatar wannan mummunan aiki na cin zarafin addini.
A nasa bangaren daya daga cikin limaman wanann yankin ya bayyana cewa abin da ya faru ya tabbatar da cewa jami’an tsaron kasar bas u gudanar da aikinsu kamar yadda ya kamata, domin kuwa ya zama wajibi wadanda suka yi hakan a kame su kuma a gurfanar da su domin fuakantar shari’a.
2831592

Abubuwan Da Ya Shafa: libya
captcha