IQNA

Gwamnatin Faransa Za Ta Yi Dubi Kan Korafin Musulmin Kasar

22:29 - February 26, 2015
Lambar Labari: 2902306
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan kasar Faransa sun ce za su yi dubi dangane da wani korafi da mabiya addinin muslunci na kasar suka gabatar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na reuters cewa, Berner Kaznov ministan harkokin cikin gidan faransa ya fadi cewa a yau ne mahukuntan kasar Faransa za su yi dubi dangane da wani korafi da mabiya addinin muslunci na kasar suka gabatar bisa la'akari da muhimmaiyar rawar da suke takawa wajen kawo zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al'ummomin kasar.

Ministan ya ce a cikin watan janairun da ya gabata an samu wasu masu tsattsauran ra'ayi a cikin kasar Faransa suna kai hari kan musulmin kasar, yayin da kuma acikin shekara ta 2014 an samu irin wannan yanayi marassa kyau, amma cewarsa suna daukar dukaknin matakan da suka dace domin kare rayukan musulmi da kuma dukiyoyinsu a kasar.

Ya ce mabiya addinin muslunci sun nuna dattijantaka matuka kana bin day a faru, domin kuwa sun nuna rashin jin dadinsu dangane da hare-haren da aka kai a kasar, a kan babu dalilin da zai sanya su kuma a dauke su matsayin abokan gaba, musulmin faransa daidai suke da kowane dan kasa, suna da dukkanin hakkokinsu nay an kasa.

Dalil Bubakar limamin masalacin Paris ya ce suna bukatar a kare dukkanin hakokinsu ba tare da nuna wani banbanci a tsakaninsu da sauran 'yan kasa ba.

2894774

Abubuwan Da Ya Shafa: France
captcha