IQNA

‘Yan Ta’addan Daesh Na Hankoron Cire Sunayen Manzon Allah Daga Masallatai

23:39 - February 27, 2015
1
Lambar Labari: 2906470
Bangaren kasa da kasa, yan ta’addan Daesh ko kuma ISIS suna wani yunkuri na cire duk inda aka rubuta sunan manzon Allah (SAW) a cikin masallatan birnin Mausil a wani mataki na shelanta yaki da manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Saumariyyah News cewa, mutanen nan yan ta’addan Daesh suna wani yunkuri na cire duk inda aka rubuta sunan manzon Allah (SAW) ko kuma wasu hotuna da ke dauke da wannan suna mai albarka a cikin masallatan birnin Mausil na kasar Iraki, a wani mataki na shelanta yaki da manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka da yan kungiyar suke shirin dauka.
Bayanin ya ci gaba da cewa tun kafin wannan loikacin dai da dama sun fara daukar matakai makamantan wannan, inda suke rusa masallatai da cibiyoyin addini da kuma wuraren tarihi, gami da kabrukan bayanin Allah da suka hada har da sahabban manzon Allah a garin na Mausil da ma sauran yankunan da suka kame iko da su.
Yan ta’addan ISIs dai sun kama yankin ne tun kimanin watanni da suka gabata tare da taimakon turkawa da kuma kurdawan kasar ta Iraki, wadanda suka hada baki da nufin karbe iko da wasu yankuna na Iraki, ta yadda su kuma za su samu damar baleewa ba tare da wani ya kawo musu wata matasala ba, amma daga bisani bayan yan ta’adda sun cimma burinsu sun koma kan kurdawa suka ci gaba da kashe su.
2904346

Abubuwan Da Ya Shafa: daesh
Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
0
allahu yatsene musu baki daya
captcha