IQNA

Azhar Ta Gargadi Kasashen Da Suke Daukar Nauyin Ayyukan Ta'addanci

23:01 - March 02, 2015
Lambar Labari: 2918919
Bangaren kasa da kasa, babban malamin cibiyar Azahar a kasar Masar Sheikh Ahmad Tayyib ya gargadi kasashen larabawa da ke baiwa kungiyoyin 'yan ta'adda taimko, da suke kaddamar da hare-haren ta'addanci da sunan jihadin muslunci.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alfajr cewa, a jiya ne  Abbas Shauman mataimakin babban malamin cibiyar Azahar a kasar Masar ya bayyana cewa Sheikh Ahmad Tayyib ya gargadi kasashen larabawa da ke baiwa kungiyoyin 'yan ta'adda taimko, da suke kaddamar da hare-haren ta'addanci da sunan jihadi das u sani cewa suna yi wa makiya muslunci aiki ne kai tsaye.
Sheikh Shauman ya bayyana cewa an wayi gari kasashen larabawa da na musulmi ne suke daukar nauyin 'yan ta'adda a bayyane, ya ce abin da 'yan ta'adda suke yin a kashe musulmi ta hanayar tayar da bama-bamaia  cikin kasar Masar da sauran kasashen musulmi da na larabawa, ba ya daga cikin koyarwar addinin muslunci.
Shehin malamin ya kirayi wadannan kasashe das u kwana da sanin cewa ko ba bade ko ba jima wadannan 'yan ta'addan za su dawo a kansu, haka nan kuma ya ja hankulan matasa da ake rudarsu da sunan jihadi suna shiga kungiyoyin 'yan ta'adda, da su koma su yi ilimi su san addinin muslunci na gaskiya wanda ya koyar da dan adam rahama da jin kai.
Ya ci gaba da cewa ya zama wajibi ga gwamnatocin da suke aikata wannan ta'ada das u gaggauta farkawa daga wannan mummunar rafkana da suke ciki, tun kafin lokaci ya kure musu, domin kuwa za su fuskanci fushin al'ummominsu a lokacin da tura ta kai bango, kamar yadda kuma za su fada a cikin fushin ubangiji.

2916543

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha