Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Yaum Sabi cewa, kamar yadda daya daga cikin mambobinta Umar Aljundi ya bayyana, daga gobe ne cibiyar Hasubiyyah cibiyar da ke gudanar da ayyuka ta fuskar kur'ani za ta fara aiwatar da wani shiri na bayar da horo kan sahihin karatun kur'ani mai tsarki da kuma inganta shi da kiyaye kaidojinsa.
Ya ce wanann shirin ba zai takaita da kyautata kira'a ba kawai, har ma zai tabo wasu bangarori da suka shafi nahwu da sauransu, domin gudanar da karatun ta hanyar mai kyau a bangaren karatu da kuma ma'ana ta larabci, ta yadda mai karatu zai san abin da yake fada a lokacin da yake karanta kur'ani tare da fahimtar da wasu.
Umar Aljundi ya kara cewa, cibiyar tana amfani da salon koyarwa da kuma horo na Mostfa Amin daya daga cikin fitattun malamin kur'ani a jami'ar Qahirah, wanda ya samu gogewa ta hanyar bayar da horo ga makaranta a kasar.