IQNA

An Gudanar Da Jerin Gwanon La’antar Daesh A Kasar Canada

23:47 - March 24, 2015
Lambar Labari: 3036056
Bnagaren kasa da kasa, an gudanar da wata zanga-zangar nuna adawa da kuma la’antar kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh a jahar Alborta ta kasar Canada tare da nisanta a bin da kungiyar ke yi da muslunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar radio-Canada cewa, a jiya a gaban majalisar dokoki wasu gungun muslumi sun gudanar da wani jerin gwanon nuna adawa da kuma la’antar kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh a jahar Alborta ta kasar Canada da ke bata sunan addinin musulunci a idon duniya.
Wadanda suka gudanar da wannan zanga-zanga sun yi imanin cewa ko shakka babu abin da wannan aiki na ta’addanci da wannan kungiya take akkatawa baya rasa nasaba da mummunar akidar kafirta musulmi da wasu kasashen larabawa suke yada a tsakanin al’umma, kuma hakan ya hadau da jahilcin musluncin, wanda matasa suke ruduwa suna shiga kungiyoyin ta’addanci da sunan jihadi ko kare sunna.
Jerin gwanon nasu ana gudanar da shi ne domin wayar da kan mutanen  mutanen kasar wadanda ba su san wani abu dangane da koyarwar muslunci ba maimakon hakan ma suna kallon wannan addini mai tsarki, a  matsayin wani addini mai dake da wata akida maras kyau wadda ake danganta ta da ta’addanci kamar dai yadda ake kallonsa a yanzu kasar da sauran kasashen turai.
Tun kafin wannan lokacin malaman addinin muslunci a kasar sun bayar da fatawoyi na haramta shigta kungiyoyin ta’addanci da ke kashe dan adam da sunan addini muslunci babu gaira babu sabar, wanda kuma hakan yana faruwa ne ta hanyar udar matasa da suka hada har matasan musulmi na wannan kasa, kuma ana yin jerin gwanon ne  ajahar Alborta saboda wata dokar ta’addanci da majalisar za ta amince da ita, mai suna C-51.
3030972

Abubuwan Da Ya Shafa: canada
captcha