Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alyaum Sabi cewa, gidan radio yahudawan Sahyuniya ya habarta cewa ana shirin gina wasu matsugunnan yaudawa cikin yankunan palastinawa dake gabacin birnin Qods.
Rahotan majalisar dinkin duniya daga ofishinta dake yankin Aucha ya habarta cewa, gidaje 30 ne mallakin palastinawa yahudawa za su rrushe bisa hujjar cewa sun saba wa ka’ida, a daidai lokacin da kuma gwamnatin haramatacciyar kasar ke shirin gina matsugunnai a wuraren.
Wanann shiri na gwamnatin sahyuniyawa yana zuwa ne duk kuwa da irin kiran da manzon musamman na majalisar dinkin duniya ya yi Benjamin Netanyahu na wajabcin dakatar da duk wani ginin matsugunnai a cikin yankunan palastinawa, wanda hakan ya saba wa dukkanin dokokin kasa da kasa.