Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizi na Al-nashrah cewa, Sheikh Naim Qasem ya bayyana ‘yan ta’addan takfiriyya wannan lokaci da cewa su ne khawarijawan zamanin da muke rayuwa.
Ya ci gaba da cewa babban abin takaici ne yadda aka wayi gari wasu daga cikin kasashen yankin kare su samu shiga wurin yahudawa, ya sanya har suna wuce gona da iri wajen kokarin biyan bukatun yahudawa, ta yadda ya zama suna hankoron rusa al’ummar musulmi duk da sunan hankoron kare manufar makiya muslunci.
Ya ce idan da sauran kasashen larabawa za su dauki darasi daga abin da yake faruwa dangan eda bangarorin da suka ki mika kai ga wadannan manufofi na makiya da bas u shiga fangima da dimuwa ba kamar yadda suke a yanzu, da kuma sun wanzu da mutunci, sabanin yadda suke yanzu a wurin al’ummominsu da kuma wurin mutanen duniya da kuma hatta wadanda suke yi domin su.
Haka nan kuma dangane da yadda suke bata rayuwar matasa suna karkatar da su zuwa ga shiga kungyoyin ’addanci da suke aikewa da su wasu yankuna da ba su dasawa da su, hakan na daya daga cikin manya kura-kurai da wadannnan gwamnatoci da masaurun larabawa suke tafkawa, domin kuwa lokaci na zuwa wanda dukkanin abin da suke shufka na sharri zai dawo a kansu baki daya, domin makiya bas u da amana.
3079861