IQNA

An Bude Wani Sabon Matsugunnin Yahudawan Sahyuniya

23:52 - April 04, 2015
Lambar Labari: 3086279
Bangaren kasa da kasa, an bude wani sabon matsugunnin yahudawan sahyuniya a cikin yankunan palastinawa da ke gabacin masallacin Aqsa.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na world Bulletin cewa, a cikin yan kwanakin nan yahudawan sahyniya sun bude wani matsugunnia  cikin yankunan palastinawa a ci gaba da ammaye yankunansu da suke yi.
Bayanin ay ci gaba da cewa wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin al’ummomin duniya da suka hada har da wasu daga cikin baiwa Isra’ila kariya suka fara juya mata baya danagne da ayyukan ta’addancin da take aikatawa a kan al’ummar palastinawa.
A nata bangaren kotun hukunta mayan laifuka ta duniya ta amunce da bukatar al'umma Falestinu na zama memba  a kotun ta kasa da kasa.
Yau laraba ne dai kotun ta duniya ta amunce a hukumance da yankin Palestinun a matsayin memba, bayan da ta mika bukatar hakan watanin baya domin kalubalantar yahudawan Israi'la gaban kotu  dake Hage akan cin zarafin bil adama, laifukan yaki da kuma mamayar da Isra'ila keyi mata.
Tuni dai Israila cikin wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin wajen ta, ta kalubalanci matakin kotun ta duniya wanda ta danganta da siyasa, inda ta ce wanan matakin da Palestinu ta dauka zai gurgunta kokarinda kasashen keyi na shawo kan rikicin daya ki ci yaki cinyewa tsakanin Israi'la da Palestinu.
3084054

 

Abubuwan Da Ya Shafa: HKI
captcha