Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Alalam cewa, Sheikh Muhammad Almunsi daya daga cikin mambobin majalisar malaman kasar Bahrain ya bayyana cewa suna gudanar da wanann jerin gwano ne da kuma taruka domin tunawa da abubuwan da suka faru na cin zarafin al’umma da kuma danne hakkokinsu.
Babbar jam'iyyar adawa a kasar ta Bahrain a cikin wani bayani da ta fitar a yammacin jiya, inda ta tabbatar da cewa an gudanar da zanga-zanga fiye da dari da hamsin a sassa daban-daban na kasar, inda akasarin al'ummar kasar suka fito suna jaddada matsayinsu na neman a gudanar da sauye-sauye a cikin salon tafiyar da mulkin kasar, ta yadda al'umma za su zama wani bangare na siyasa.
Maimakon mulkin mulukiya na danniya a kan al'umma, a ranar sha hudu ga watan fabrairu shekatra ta dubu biyu da sha daya al'ummar Bahrain suka fara gudhrain suka fara gudanar da ekara taanar da sauye-sauye a cikin salon tafanar jerin gwano da gangami domin neman sauyi ta hanyar lumana, inda mahukuntan kasar suka nemi taimakon kasashen ketare domin murkushe fararen hula a kasar da ke jerin gwano na lumana, inda suka kashe da tare da jikkata mutane da dama.