Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alfajr cewa, Abbas Shuman mataimakin cibiyar Azahar ya bayyana cewa, Shehin Azhar din ya bayyana cewa sakon addinin muslunci na duniya ne baki day aba na ta wata kungiya ko wani bangare ne kadai daga cikin al’umma ba.
A bangare guda kuma babban malamin jami’ar Azhar ta kasar Masar ya zargi wasu kasashen yammacin Turai da na Larabawa da hannu a goyon bayan ayyukan ta’addanci a kasar ta Masar, a jawabinsa babban Sheikhin jami’ar Azhar Sheikh Ahmad Tayyib ya bayyana cewar wasu kasashen yamma da ‘yan koransu na kasashen Larabawa ne suka cunawa kasar Masar ‘yan ta’adda kuma da kudaden irin wadannan kasashe kungiyoyin ‘yan ta’adda suke ci gaba da aiwatar da munanan ayyukansu na kashe-kashen rayuka da barnata dunkiyar al’umma.
Sheikhin Azhar ya kara da cewar maha’inta da shaidan ya hurewa kunne suke daukan nauyin ayyukan ta’addanci a Masar. A hare-haren ta’addancin baya bayan nan da aka kai kasar ta Masar sun yi sanadiyyar mutuwan jami’an tsaron kasar da fararen hula kimanin talatin tare da jikkatan wasu da dama a yankin Sina. A bayan kai hare-haren shugaban kasar Masar ya bada umurnin kafa wata runduna da zata dauki alhakin yaki da ta’addanci a kasar.
Babban malamin cibiyar Azahar a kasar Masar Sheikh Ahmad Tayyib ya gargadi kasashen larabawa da ke baiwa kungiyoyin 'yan ta'adda taimko, da suke kaddamar da hare-haren ta'addanci da sunan jihadin muslunci. Sheikh Ahmad Tayyib ya bayyana cewa an wayi gari kasashen larabawa da na musulmi ne suke daukar nauyin 'yan ta'adda a bayyane, ya ce abin da 'yan ta'adda suke yin a kashe musulmi ta hanayar tayar da bama-bamaia cikin kasar Masar da sauran kasashen musulmi da na larabawa, ba ya daga cikin koyarwar addinin muslunci.
Shehin malamin ya kirayi wadannan kasashe das u kwana da sanin cewa ko ba bade ko ba jima wadannan 'yan ta'addan za su dawo a kansu, haka nan kuma ya ja hankulan matasa da ake rudarsu da sunan jihadi suna shiga kungiyoyin 'yan ta'adda, da su koma su yi ilimi su san addinin muslunci na gaskiya wanda ya koyar da dan adam rahama da jin kai.