Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almisriyun cewa, Tsivi Mazal tsohon jakadan haramtacciyar kasar Isra'ila a kasar Masar ya yaba tare da nuna jin dadinsa matuka dangane da cire ayoyin kur'ani masu magana kan Jihadi da shugaban kasar Masar Abdulfattah Sisi ya yi a cikin amnhajar karatu.
Ya ci gaba da cewa hakika abin da Sisi ya yi gagarumin aiki ne wanda zai kawo sauyi mai matukar muhimmanci a cikin tsarin karatun kasar Masar, kama daga mataki na farko har zuwa jami'oi, domin kuwa zai dakushe yaduwar tuannin kaifin kishin addini wanda kan kai matasa zuwa ga ayyukan ta'addanci.
Tsivi Mazal ya kara da cewa abin da shugaban na masar ya yi hakia wani abu ne da ake bukata a cikin wannan lokaci a kasar ta masar, domin kuwa akwai bukatar a kawo gyara a cikin manjar karatun da cibiyar Azahar ta amince da shi a kasar, domin samun fahimta tsakanin dukkanin mabiya addinai da aka safkar daga sama.
An rubuta wannan bayani ne a cikin wata makala da ya rubuta da aka buga, wadda ta samu yabo daga manyan yahudawan Israila, da suka hada har da Dorry Gold, daya daga cikin na hannun damar Netanyahu, wanda ya ce wanann makala ta yi kyau matuka.
3185606