Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na lefaso.net cewa, wannan zaman ya jadda wajabcin rayuwa tare da juna tsakanin musulmi da kirista da ma dukaknin mbaiya addinai na kasar ta Burkina faso baki daya.
Shi dai wananna zaman taron da cibiyar bunkasa al’adun muslunci ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa, ya hada dukaknin bangarori na mabiya addinai a kasar, muasamman ma dai mabiya addinai kiristanci da muslunci da ke bin Kur’ani da Injila wadanda su ne suka fi yawa atsakanin al’ummar kasar.
Inda dukkanin bangarorin suka maince da cewa babu wani abu da ya fi zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsu, ta yadda kowa zai yi addininsa bisa fahimtarsa a lokaci gda kuma a na zaune lafiya da juna ba tare da wani tashin hankali ko takura ma wani bangare ba.
Imam Tim Toure daya daga cikin wadsanda suka gabatar da jawabi ya bayyana cewa, rayuwa tare da juna cikin zaman lafiya na daya dsaga cikin koyarwar kur’ani da sunnar manzo (SAW) da suka koyar da musulmi.
Shi ma Sawadugu daya daga cikin limaman kiristanci da ya halarci wurin ya bayyana cewa, ko shakka babu zaman lafiya da fahitar juna da saurana ddini na daga cikin koyarwar Injila ga mabiya addinin kiristanci.