IQNA

An Gudanar Da Zanga-Zangar Neman Sakin Sheikh Nimir Fursunonin Siyasa A Saudiyyah

23:13 - May 08, 2015
Lambar Labari: 3274327
Bangaren kasa da kasa, dubban mutane sun gudanar da zanga-zangar a yankin Awamiyyah da ke gabacin Saudiyyah na yan shi’a domin neman a saki Ayatollah bakir Namir da sauran fursunonin siyasa akasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Masdarak News cewa, an gudanar da zanga-zangar lumana a kasar yankunan Awamiyya da ke gabacin kasar Saudiyya, da ke neman a saki Sheikh Namir da sauran  fursunonin siyasa da mahukuntan kasar ke tsare da su.

 

Masu zanga-zangar sun fit one duk kuwa barazanar da mahukuntan kasar saudiyya suka yi kan shiga kafar wando daya da duk wanda ya gudanar da wata zanga-zanga ko gangami da ke kalu balantar mahukuntan kasar.

Dubban jami'an tsaro ne a cikin kayan sarki suka isa yankunan daban-daban da ke gabacin Saudiyya, domin hana gudanar da irin wannan zanga-zanga, amma duk da hakan al'ummomin yankunan Al-awamiyya sun fito kan tituna, dauke da hotunan daruruwan mutanen da gwamnatin saudiyya take tsare da su tsawon shekaru saboda dalilai na siyasa, ba tare da gurfanar da su gaban kuliya ba.

 

A wani mataki na yunkurin kaucewa boren al'umma kamar yadda ya faru a kasashen larabawa kuma yake ci gaba da faruwa a kasashen larabawa da dama, mahukuntan kasar Saudiyya sun sha alwashin kyautata rayuwar talakawa, tare da kara samar da guraben ayyuka ga masu zaman kashe wando a kasar. 
3272200

Abubuwan Da Ya Shafa: saudiyya
captcha