Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Muslim Village cewa, yanzu haka dai mabiya addinin muslunci a kasar Australia sun bude wata sabuwar hanya ta Facebook domin yada addinin muslunci ta hanyar yanar gizo da nufin fahimtar da wadanda ba su da masaniya ko kuma suke da karancinta dangane da musulunci.
Bayanin ya ci gab ada cewa muhimamn abubuwan da wannan shafi zai mayar da hankali knasa shi ne, yadda zai bayyana matsayin addinin muslunci da kuma yadda yak ekallon sauran batutuwa da suka shafi zamantakewa tare da sauran addinai, kasantuwarsa addini ne na zaman lafiya da kyautata zamantakewa.
Mabiya addinin muslunci a kasar Australia dai na daga cikin msuulmi da suke samun kula da hakkokinsu idan a ka kwatanta da sauran wasu kasashen turawa, inda musulmi suke fuskantar matsaloli masu tarin yawa na wariya da kuma kyama da ake nuna musu a cikin dukkanin lamurransu na rayuwa.
Wanda ya kirkiro da shafin y ace yana fatan har ma manyan jami’ai na kasar da suka hada da yan siyasa za su amfan ada wannan shafi, ta hanyar yin amfani da shi domin sanin muslunci da kuma abubuwan da yake koyarwa kuma yake yin kira zuwa gare su, maimakon dogaro da abubuwan da ake fada kan musulunci marassa tusheda kan gado.
3304555