IQNA

An Aike wa Wasu Masallatan Amurka Wasikun barazana

20:42 - May 28, 2015
Lambar Labari: 3308732
Bangaren kasa da kasa, an aike da wasu wasikun da ke yi barazana ga wasu masallatai na musulmi a cikin jahar Arizona ta kasar Amurka.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ABC News cewa, wannan wasika an aike ta zuwa ga kungiyar musulmi da finks da kuma kungiyar jam’iyyar musulmi ta yankin.

Majalisar musulmi ta kasar Amurka ta aike da lauyanta zuwa ga hukumar yan santa masu gudanar da bincike kan manyan laifuka na FBI domin tattauna lamarin.

Usama Shami shugaban cibiyar musulmi na yankin ya bayyana cewa, an aike da wannan wasika zuwa ga cibiyar, amma kuma ana yin barazana ne ga masallatai.

Ya ce suna gudanar da harkokinsu a cikin masallatansu ba tare da wata matsala ba, kuma ba su taba tsokanar wani ba, sai ga shi kuma su ana tsokanarsu kai tsaye.

Yanzu haka dai yan sanda a yankin sun dauki matakai na gudanar da bincike kan wannan lamari, domin shawo kansa kafin ya kai ga wani mataki na wuce gona da iri.

3308583

Abubuwan Da Ya Shafa: amurka
captcha