Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na aynar gizo na Al-wifagh cewa, majalisar dinkin duniya da kuma kungiyar kare hakkin bil-Adama ta duniya sun bukaci hanzarta sakin jagoran ‘yan adawar kasar Bahrain Sheikh Ali Salman.
A bayanin da kungiyar kare hakkin bil-Adama ta fitar yana dauke da sanarwar cewa; mahukuntan gidan sarautar Bahrain suna tsare da Sheikh Ali Salman babban sakataren jam’iyyar Al-Wefaq kuma jagoran ‘yan adawar kasar ne saboda furta albarkacin bakinsa ta hanyar lumana, don haka tana kira ga mahukuntan Bahrain da su hanzarta sakinsa ba tare da gindaya wani sharadi ba kuma a cikin gagagwa.
Ba a da bayan haka kungiyar bukaci gidan sarautar Bahrain da ta mutunta hakkin furta albarkacin baki da duk wani yunkurin ‘yan adawa ta lumana tare da kawo karshen dokokin da suka hana kafa kungiyoyi da jam’iyyun siyasa a kasar ta Bahrain.
Kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa sun kwatanta gidajen kason kasar Bahrain da gidajen kason gwamnatin 'yan wariya a kasar Jamus karkashin jagorancin fitaccen shugabandu..
Tsar Sheikh Ali Salman ya kara tabatar wa da duniya cewa mahukuntan wannan kasa yan mulkin kama karya ne da ba su son zaman lafiya, illa dai kawai yin amfani da karfi kan duk wanda ya nemi yay a nuna musu kurensu, saboda suna ganin al’ummar kasar mallakinsu, abin da Sheikh Salma da sauran yan adawa ba su amince da shi ba.
3312239