Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Shafana cewa, yan shi’ar kasar Masar sun bayyana cewa ba za su kara boye wani abu dangane da lamarinsu ba tare da karyata vcewa sun yi taron maulidin Imam Hujja (AS) a boye domin tsoro, inda suka babu wani dalili na yin hakana cikin sirri.
Hashemi y ace tun kafin wannan lokacin an jima ana danganta lamurra da dama da su, amma kuma suna ci gaba da yin hakuri, duk kuwa da cewa yanzu lokaci ya yi da za su ci gaba da yin komai a bayyane kamar yadda kowa ke yin komai a bayyanae a kasar daidai da koyarwar addininsa ko akidarsa.
Shi ma a nasa bangaren Dr. Rasim Nafis ya ce su yan kasa ne kamar yadda kowane dan kasa yake, babu wani mutum wanda ya fi su zama dan kasa, saboda hakka babu wanda yake da hakki a Masar wanda su ab su da shi, saboda hakan daga yau ta kare, komai nasu a bayyane yake, wanda yake bukata ya ji abin da suke fada yana iya zuwa, wanda bai bukata kuma ya kama gabansa.
A cikin yan kawanakin nan ne wasu masu adawa da shi’a a kasar ta Masar suke yada cewa yan shi’a sun yi maulidin Mahdi (AS) a boye saboda tsoro.
3313458