IQNA

Wakilin Iran A Gasar Kur’ani Ta Malaysia Ya Cancanci Matsayin Da Ya Samu

17:53 - June 15, 2015
Lambar Labari: 3314809
Bangaren kasa da kasa, Dukkanin alkalan da suka yi alkalanci a gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasar Malaysia 15 da suka hada 5 daga Masar, sun bayyana cewa wakilin Iran ya cancanci matsayin da ya samu a gasar.


Mohamamd Reza Pour Moen shugaban cibiyar kur’ani mai tsarki a Tehran a lokacin kamala gasar a zantawa da wakilin Iqna a Kualalampour ya bayaynaa cewa, da farko dai yana taya al’ummar kasar Iran murnar samun wanann nasara baki daya.





Y ace wakilin Iran ya samu fiye da maki 7 inda ya zama banbancinsa da mai bye masa na da yawa, ya samu maki 95.5 yayin da mai biye masa ke da maki 88.5, duk kuwa da cewa dan akasar kuma dan kabilaMalayu.

Dangane da Hasani Kargar kuwa, ya bayyana cewa hakika wannan makaranci ya nuna kwazo matuka, kuma matsayin da ya samu ya tababtar da cewa kwaonsa ne da kuma himma da ya nuna, bayan shekaru 9 Iran ta sake samun matsayi na daya bayan lashe gasar.

Bayanin nasa ya ci gaba da cewa abubuwan da suka faru a wajn gasar suna koyar da darussa masu tarin yawa, daga ciki kuwa har da kawar da kaia daga komai, tare da sanya buri a gaba kawai da kuma yindogaro ga Allah, domin hakan shi ne sirrin duk wata nasara a cikin lamurra.

Alkalan da suka yi alkalanci a gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasar Malaysia 15 ne da suka hada 5 daga Masar, amma duk da haka ya sau matsayi na daya.

3314385

Abubuwan Da Ya Shafa: malaysia
captcha