IQNA

Kungiyar ISESCO Ta Yi Allawadai Da Gerrt Wilders Kan Zanen Batunci

23:52 - June 21, 2015
Lambar Labari: 3316988
Bangarn kasa da kasa, kungiyar raya al’adun muslunci ta duniya ta yi Allawadai da kakkausar murya dangane da sake yada zanen batunci kan ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da ya yi a Youtube.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ISESCO cewa, Abdulaziz Usman Al-tuwaijari shugaban kungiyar raya al’adun muslunci ta duniya y ace kungiyar ta yi Allawadai da kakkausar murya dangane da sake yada zanen batunci kan ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi (SAW) da ya yi a cikin kwanakin nan.

A bangare guda kuma wata kotu a amsterda baban birnin kasar ta ce dole ne a hukunta Geert Wilders dan majalisa mai cin zarafin addinin Musulunci.

Kotun daukaka kara ta birnin ta bada umurnin a gurfanar da Geert Wilders bisa zargin cewa maganganun batunci ga Musulmi da addininsu da ya yi a kafafen watsa labarai suna tunzura mutane don su nuna kiyayya da bambamci ga wasu jama'a.

Masu shigar da kara sun sami kiraye-kiraye masu yawa na bukatar a duganar da bincike saboda wani fim da Wilders ya shirya wanda ya kira fitna" da kuma maganganun ya yi a jaridu, wadanda suka hada da inda ya kwatanta kur'ani mai girma da Mein Kampf littafin da itler ya rubuta, ya kwatanta addinin Musulunci da akidar Nazi.

Wannan aiki na dan majalisar kasar Holland din ya fuskanci maida martani mai tsanani daga al'ummar Musulmi, duk kuwa da cewa wasu daga cikin shugabannin kasashen larabawa musamman ma masu raya cewa suna bin tafarkin snna sun gum da bakunansu.

3316656

Abubuwan Da Ya Shafa: isesco
captcha