Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na On Islam cewa, a wannan shekara musulmin kasara Canada kamar sauran wurare da ke arewacin duniya, suna yin azumi mai tsawon gaske.
Bayanin ya ce alfijiri kan fito kimanin karfe 3:45 na dare yayin da kuma ranar ta kan kai karrfe 9 na yamma kafin ta fadi, wanda hakan ya sanya za su yi azumi na tsawon saoi goma sha bakwaia kowace rana a cikin wannan wata mai alfarma.
Duk da tsawon lokacin da kuma kasantuwar suna rayuwa acikin wata kasa wadda ba ta mabiya addinin muslinci ba, amma duk da hakan kuma suna daurewa tare da karfin imaninsu su yi azumin ba tare da nuna wata damuwa ba.
Khalil Khalilof daya daga cikin muslmi mazauna yankin North York ya bayyana cewa, wannan shi ne karo na farko da yake yin irin wananna zumi mai tsawon gaske, amma kuma duk yadda rana ta yi tsawo dole ne ya yi azumi, domin daya ne daga cikin ayyukan farillada ubangiji ya wajabta.
Yawan musulmin kasar Canada ya karu kashi 80% cikin dari idan aka kwatanta da sauran shekaru goma da suka gabata, inda a wancan lokacin daga mutane 579000 a cikin shekara ta 2001 ya haura zuwa fiye da miliyan daya, al’mmar msulmi a Canada sun kai kashi 04% na dukkanin al’ummar kasar a halin yanzu.
3318279