IQNA

Za A Kori Limamai Masu Yada Tsatsauran Ra’ayi A Kasar Algeria

20:20 - July 01, 2015
Lambar Labari: 3322223
Bangaren kasa da kasa, minister mai kula da harkokin addinin muslunci a kasar Algeriya ya bayyana cewa za su dauki dukkanin matakan da suka dace domin korar limamai masu yada tsatsauran ra’ayi.


Kamfanin dilalndcin labaran iqna ya nakalto daga bangaren yada labaransa na Afirka cewa, Muhammad Isa minista mai kula da harkokin addinin muslunci a kasar Algeriya ya bayyana cewa za su dauki dukkanin matakan da suka dace domin korar limamai daga masallatai masu yada tsatsauran ra’ayin addini a kasar.

Ministan ya ci gaba da cewa yanzu haka an kafa wani kwamiti wanda zai sanya ido a kan dukkanin harkokin masallatai a kasar da jin irin abubuwan da malamai suke fada, da kuma irin lamurran da ake gudanarwa a cikin masallata.

Ya ce yanzu haka an bayar da sunayen wasu limamai guda 55 da suke yada akidar nan ta kafirta musulmi a kasar a cikin masallatansu, wanda hakan yasa ala tilas a dakatar da su kuma a hana gudanar da duk wasu lamurra a cikin masallatai.

Wannan mataki dai ya zop sakamakon irin lamurran da suke faruwa na ta’addanci a cikin kasashen larabawa musamman ma a kasashe da suke makftaka da kasar, inda ake kai hare-haren ta’addan sakamakon yaduwar akidar kafirta muuslmi.

3321755

Abubuwan Da Ya Shafa: aljeria
captcha