Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alseraj cewa, a jiya ne aka bude wata gasa ta karatun kur’ani mai tsarki da kuma ilmomin addinin muslunci, a Nuwakshot tare da halartar Ahmad Wuld Ahlu Dawud minister mai kula da harkokin addini na kasar Mauritaniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa, baya ga halaratr manyan jami’an gwamnati da suka hada da ministan, an kuma samu halartar dalibai da kuma malamai daga sassa daban-daban na kasar, domin bayar da gudunmawa ko dai ta fuskar shiga a ciki, ko kuma ta fuskar alkalanci.
Wannan gasa ta kasar Mauritaniya mai taken gasar kur’ani da ilmin shari’a, za a ci gaba da gudanar da ita har tsawon kwanaki gomamasu zuwa, yayin da kuma dalibai 264 ne suka halarta.
Daga karshe za a bayar da kyautuka ga wadanda suka lashe daga mataki na daya zuwa na biyar a bangarorin kr’ani, hadisi, fikihu, da kuma sira da harshen larabaci.
3322292