IQNA

Rikicn Banbancin mazhaba A Tsakanin Musulmi Yana Amafanar Da Sahyuniyawa

23:51 - July 11, 2015
Lambar Labari: 3326796
Bangaren kasa da kasa, Sheikh Ahmad karimah daya daga manyan malaan addinin muslunci a cibiyar Azahar ya bayyana rikicin banbancin mazhaba da cewa yahudawam sahyuniya kawai ke afana da shi.


Kmafanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sadal Balad cewa, Sheikh Ahmad karimah wanda daya ne daga manyan malaman addinin muslunci a  bangaren shari’a da fikihu a cibiyar Azahar ya bayyana rikicin banbancin mazhaba da kawo batun shi’a da salafawa ke yi da cewa yahudawam sahyuniya kawai ke afana da shi ba muuslmi ba.

Ya ci gaba da cewa abbu wani dalii da zai sanya musulmi su manta da muhimman lamurran da ke gabansu da za su taimaka wajen ci gaba addinin a duniya, da zai saya su dauki batun mazhaba da banbancin fahimta su zama shi ne aikinsu kawai.

Dangane da masu hankoron ganin sun fitar da wani babban bangare na musulmi daga cikin addinin kuwa wato mabiya tafarkin italan gidan manzo, ya bayyana hakan da cewa babban kure da ya kamata musulmi su sani kuma su magance.

Ta fuskar hankoron da makiya suke yi wajen ganin sun cimma buinsu na raunana musulmi, ya bayyana cewa dole ne musulmi su zama cikin fadaka, domin yahudawan sahyuniya suke amfana da rarraba tsakanin muslmi.

3326648

Abubuwan Da Ya Shafa: azhar
captcha