IQNA

Kungiyar ISESCO Ta Marhabin Da Kafa Kungiyar Malamam Afirka A Morocco

23:13 - July 16, 2015
Lambar Labari: 3328843
Bangaren kasa da kasa, Abdulaziz bin Usman Al-tuwaijaroi babban sakataren kungiyar bunkasa al’adu ta kasashen musulmi ya yi marhabin da kafa babbar cibiyar malaman muslunci a Morocco.


Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na ISESCO cewa, babban sakataren kungiyar ya yi marhabin da kafa babbar cibiyar malaman muslunci a Morocco wadda sarkin Muhammad na shida ke kokarin kafawa.

Wannan bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar kafa wannan cibiya karkashin sarki Muhammad na biyu dai ita ce, hada kan dukkanin malaman nahiyar Afirka a wuri guda, domin aiki tare wajen fuskantar kalu bale da ke a gaban mabiya addinin muslunci a cikin wannan nahiya.

Bayanin ya kara da cewa daga cikin irin wannan kalu bake kuwa har da yadda ake samun yaduwar ayyukan ta’addanci a cikin kasashen musulmi, wanda kuma hakan yak an bar mummunan tasiria  tsakanin musulmi musamman ma matasa daga ciknsu, wadanda ba su da masaniya kan addinin muslunci.

A wannan cibiyar za a mayar da hankali wajen ilmantarwa, sanan kuma akwai wayar da kai dangane da sanin hakikanin addini muslunci, da kuma sanin yadda ya kamata musulmi su tunkari mumanan akidu na ta’addanci da ake shigo da su a cikin musulmi a halin yanzu a duniya.

Sa’annan kuma dukaknin bangarorin na malaman kasashen Afika da na Morocco za su aiki tare domin yada al’adun muslunci da kuma koyarwarsa tsakanin sauran al’ummomin nahiyar da ba su da masaniya wannan addini a cewar bayanin da aka fitar.

Kiyaye akida da hana karkatar da matasa daga sahihin tafarki na addini ne shi ne dai babban manufar kafa wanann babbar cibiya ta malaman addinin a wannan nahiya.

3328384

Abubuwan Da Ya Shafa: isesco
captcha