IQNA

A Yau Za A Bude Wani baje Koli Na Kayyakin Addinin Muslunci A Italia

22:04 - July 24, 2015
Lambar Labari: 3332513
Bangaren kasa da kasa, a yau ne za abude wani babban baje koli na kayyakin al’adu da tarihin muslunci a cibiyar Scodray Del Covirinal da ke birnin Rom na kasar Italia.


Kamfanin dilalncin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto dagabshafin sadarwa na yanar gizo na kasar Kuwait cewa, wannan babban baje koli na kayyakin al’adu da tarihin muslunci zai gudana ne bisa daukar nauyin cibiyar adana kayan tarihin muslunci ta Kuwait.

Bayanin ya ci gaba da cewa an gudanar da irin wannan baje koli har sau biyu a wannan wuri, kuma ya kayatar kamar yadda ake bukata, kuma a wannan karon ma ana sa ran zai fi loktan baya, bisa la’akari da irin shirin da aka yi da kuma abubuwan da aka tanada da za a nuna a wurin.

Akwai kayyaki kimanin 363 daka tanada da ska hada kayan tarohi na muslunci da suka jima na tsawon daruruwan shekaru, kamar yadda kuma za a nuna wasu daga cikin irin littafa na addini wadanda s ma sun ji a da rubutawa da ska bayyana dadadiyar alama ta tarihin muslunci.

Wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin kasar Kuwait da suka hada har ministan kula da al’adu na kasar duk da zsu samu halartar bude wannan bababn baje koli a kasar.

An zabi wanann loaci ne dai domin gudanar da wannan baje koli a wannan wuri, saboda la;’akari da cewa shi ne lokacin da yafi cika da jama’a saboda hutun bazara da miliyoyin mutane suke zuwa wurin, wanda kuma za su bukaci sanin irin wadannan abubuwa.

Wasu daga cikin wadannna kayayykin na tarihin muslunci sun bata tn tsawon shekaru, kamar yadda kuma wasu suka lalace saboda tabin ruwa ko kuma sakamakon yake-yake da aka yi ta fama da su a cikin yanknan muslunci a daruruwan shekarun da suka gabata.

3332336

Abubuwan Da Ya Shafa: italia
captcha