IQNA

Yahudawan Sahyuniya Sun kai Farmaki Kan Masallacin Quds Mai Alfarma

23:19 - July 26, 2015
Lambar Labari: 3335536
Bangaren kasa da kasa, daruruwan yahudawan sahyuniya sun kai farmaki a yau kan masallacin Quds mai alfarma bisa hujjar tunawa da wani wurin ibadarsu da suke rayawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa, da jijifin safiyar yau ne daruruwan yahudawan sahyuniya sun kai farmaki a yau kan masallacin Quds mai alfarma tare da fakewa da hujjar tunawa da wani wurin ibadarsu da suke rayawa suna da shi a zamanin da da aka rusa musu.

 

Yahudawan sun shiga masallacin ne mai alfarma domin tsokana, kuma suka ci gaba da lakada wa musulmi duka da suke a wurin, lamarin da ya harzuka muslmin suka ci gaba da kokarin hana su gudanar da abin da suke son yi, amma a nan take sojoji da ‘yan sanda Isra’ila suka kawo musu dauki, inda suka shiga antaya barkonon tsohuwa kan musulmi da ke cikin masallacin.

Majiyar palasdinawa ta bayyana cewa rikici ya tashi ne a cikin masallacin bayan da wasu yahudawa sun shigo cikin masallacin a safiyar yau, inda suke gudanar da bukukuwan tunawa da ranar da suka kwace gabacin birnin Qudus a hannun larabawa a yakin shekara ta sittin da bakawai.

 

Wani wanda ya ganewa idanunsa ya bayyana cewa jami’an tsaron yahudawan sun yi amfani da albarusai na roba da kuma hayaka mai sa hawaye kan Palasdinawa masu zanga zangar yin tir da shigowar yahudawan cikin masallacin.

Masallacin Al-Aqsa dai ya zama dandalin fada a cikin yan watannin nan, don kokarin da yahudawan suke yi na sauya yanayin masallacin zuwa mai kamannin yahudanci. Har’ila yau akwai shirin gina wurin bautar yahudawa a cikinsa.

 

3335343

Abubuwan Da Ya Shafa: quds
captcha