IQNA

Karancin Kudi Ne Babbar Matsalar Makarantun Kur’ani A Nijar

23:52 - July 27, 2015
Lambar Labari: 3335983
Bangaren kasa da kasa, karancin kudi shi ne abbar matsalar makarantun kur’ani da suka kai kimanin dubu 50 a kasar Nijar.


Kamfanin dilalncin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin saarwa na yanar gizo na Peninsula cewa, a halin yanzu karancin kudi shi ne abbar matsalar makarantun kur’ani a Nijar wadanda wasunsu suna karatu ba tare da ajujuwa ba, amma duk da hakan wannan bai saya sun dakatar da karatun ba.

Bayanin ya ci gaba da cewa makarantu a kasar suna da yawan gaske, wanda ya kai dubu hamsin ko fiye da hakan a kasar, amma kuma suna fuskantar matsaloli masu tarin yawa, wadanda suke da alaka da matsalar kudaden tafiyarwa.

Da dama daga cikin irin wadannan makarantu suna mayar da hankali ga karaun kur’ani mai tsarki da kuma sanin kaidojin karatu, kamar yadda wasu daga cikinsu suke hada wa har da wasu ilmomi na addini da suka hada da tafsirin kur’ani mai tsarki.

Mamalai suna samun horoa  wasu daga cikin kasashen larabawa da ke makwaftaka da kasar a fannin ilmomin kur’ani da ak ekoyarwa a cikin wadannan makarantu, wanda hakan ya taimaka matuka wajen yada wannan ilmi.

Wasu daga cikin kungiyoyin alkhairi na kasashen larabawa musamamn Qatar suna taimakawa matuka domin tabbatar da cewa wannan shiri ya samu karbuwa inda suka gina cibiyoyi 169na kur’ani a tsakanin al’ummar kasar.

Wannan cibiya kuma tana daukar nauyin kula da wadanna cibiyoyi na koyar da karatun kur’ani mai tsarki da ta gina tare da biyan malamansu.

3335644

Abubuwan Da Ya Shafa: nijar
captcha