Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na The Local cewa, wasu yan majalisar dokokin jahar Torin a kasar Italiya sun bukaci da akwace dukkanin dardumomi da musulmi suke yi amfani da su wurin yin salla.
Wannan bukata da yan majalisar biyu suka mika ta jawo kakkausar daga mabiya addinin muslunci na kasar ta Italiya da ma wasu daga cikin wadanda ba musulmi ba, da suke ganin hakan ya sabawa kaida ta dimokradiya da da kasar ke tafiya a kanta.
Domin mayar da martini kan wannan lamari wasu daga cikin yan majalisar da suke sukar kudirin, sun bukaci da a gudanar da wani baje koli n akayyakin muslunci a babban ginin karamar hukumar birnin, domin nuna goyon bayansu ga musulmi.
Yanzu haka dai wasu daga cikin al’ummomin kasar sun dauki matakin bin hanyoyi na doka domin kalubalantar wannan bukata, domin suna ganin cewa yin hakan zai zama takura ma wani bangare ne na al’ummar kasar.
Shi ma a nasa bangaren shugaban majalisar dokokin yankin ya bayyana cewa ba zai amince da wannan bukata ba, domin kuwa ta yi hannun riga da koyarwa da tadimokradiyya da kare hakkokin marassa rinjaye.
3336767