IQNA

Babu Dalilin Kafirta Mabiya Shi’a A Kur’ani Mai Tsarki Da Kuma Sunna

20:28 - August 07, 2015
Lambar Labari: 3339769
Bangaren kasa da kasa, Ahmad Tayyib babban malamin cibiyar Azhar ya bayyana cewa babu wani dalili na kafirta mabiya mazhabar shi’a a cikin kur’ani mai tsarki da sunnar manzon Allah da wasu tashoshi suke yi.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-nakhil Irak cewa, Ahmad Tayyib ya bayyana cewa dangane da wannan batu, suna yin salla a bayan yan shi’a suma suna yin salla a bayansu, saboda haka babu wani sabanin tsakanin sunna da shi’a da zai kai har ga kafirta wani bangare.

Ya ce idan ya yi tafiya zuwa Iraki zai kai ziyara zuwa birnin najaf domin haduwa da manyan malaman shi’a, saboda babu wani dalili na kafirta mabiya mazhabar shi’a a cikin kur’ani mai tsarki da sunnar manzon Allah da wasu tashoshi suke yi a kullum domin haifar da fitini tsakanin al’umma.

Sheikh Ahmad Tayyib ya ce aiki na farko da ke gaban cibiyar Azhar a halin yanzu shi ne hankoron ganin an samu hadin kai tsakanin dukkanin al’ummar musulmi, wanda hakan ya hada dukkanin bangarori na musulmi baki daya, ba tare da ware wani bangare ba.

Sheikul Azhar ya cea  kwanaki baya ya gana da wata tawaga daga kasar Iraki, wadda ta kunshi dkkanin bangarori na musulmin kasar, saboda haka shi ma nan ba da jimawa ba zai tafiya zuwa kasar Iraki, kuma zai gana da dkkanin bangarori, kamar yadda yattabar da cewa shi baba ne ga sunna da kuma shi’a.

Ya kara da cewa a halin yanzu cibiyar Azhar tana yin iyakin kokarinta domin tabbatar da hadin kan al’ummar musulmi, tare da fuskantar babbar matsala ta shigo da munan akidu na kafirta  amusulmi da ke haifar da ta’addanci da sunan muslunci a halin yanzu.

3339682

Abubuwan Da Ya Shafa: azhar
captcha