IQNA

Za A Bayar da Horo Kan sanin Sunayen Allah 99 A Birnin London

21:54 - August 21, 2015
Lambar Labari: 3349570
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani shiri na bayar da horo kan sanin maanoni na sunayen Allah madaukakin sarki guda 99 a birnin London.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na iidr cewa, ana shirin gudanar da wani shiri na bayar da horo kan sanin maanoni na sunayen Allah madaukakin sarki guda 99 da nufin kara fito da ma’anarsu ga mabiya addinin muslunci da suke da sha’awar sanin hakan.



Wannan horo dai zai hada mabiya addinin muslunci daban-daban da suke son sanin manoni da falsafar wadannan sunaye masu tsarki da albarka, kasantuwar hakan ya zama sane a wajen musulmin kasar cewa suna bayar muhimmanci ga wadanan sunaye.



Daga cikin abin da horon zai kunsa har da yadda mutum zai amfana da wadanann sunaye wajen samun kusanci da Allah madaukakin sarki, domin kuwa kowane daya daga cikin sunayen Allah yana da matsayi da kuma hanyar yin amfani da shi domin samun kusannci da Allah.



Shirin dai zai gudana ne karkashin cibiyar gudanar da bincike kan addinin muslunci da kuma ilmominsa kamar dai yadda bayanin ya yi nuni.



Hamd Arrahmani Fahim mahardacin kur’ani mai tsarki kuma malami a wata makaranta a garin Manchester shi ne zai dauki nauyin bayar da horon da kansa ga musulmin da suka yi rijistar sunayensu.



3347195

Abubuwan Da Ya Shafa: birtaniya
captcha