IQNA

Zargin Iran Da Kokarin yada Shi’a A Masar Ba Shi Da Wani Asasi

23:57 - August 22, 2015
Lambar Labari: 3350068
Bangaren kasa da kasa, Sheikh Abdullah Nasr daya daga cikin malaman kasar Masar ya karyata abin da yan salafiyya ke fada na cewa Iran na kokarin yada amzhabar shi’a a Masar.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Shafaqna cewa, sheikh Abdullah Nasr daga aka fi sani da Sheikh Mizu, bayana halartartar taruka a Iran da kuma Lebanon ya bayyana cewa, babu wani dalili na cewa Iran na kokarin yada mazhabar shi’a a cikin kasar kamar yadda yan salafiyya da masu adawa da Iran suke ikirari.

Malamin ya ci gaba da cewa bayan samu gayyata daga malaman Haza na halarci tarukansu kuma na ji abin da suke fada babu gaskiya kan cewa suna kokarin yada mazhabarsu, kamar yadda kuma malaman shi’a shi’a suna fitar da fatawa ta hana zagin sahabbai da matan manzon (SAW)

Haka nan kuma malana shi’a a shirye suke su karba kiran da babban sheikhul Azhar ya yi na zama kan teburin tattanawa tsakanin malaman shi’a a da sunna domin warware rashin fahimtar juna.

Ya kara da cewa yan salafiyya suna yada karya kan Iran da cewa tana son yada mazhabar shi’a  aMasar, wanda babu gaskiya a hakan, ya ce idan son Ahlul bait (AS) shi ne shi’a to dukkanin mutanen Masar yan shi’a ne.

3349627

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha