Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na On Islam cewa, Sultan Kuraishi babban jami’i mai kula da ayyukan gyaran masallaci mai alfarma ya ce da yardarm ubangiji za a kammala aikin hawa na hdu na dakin Ka’abah da masallacin manzo (SAW) kafin fara aikin hajjin bana.
Ya ce a halin ynzu an kammala hawqa na uku da fadin mita murabba’i dubu 76 na zagayen fadin baki daya.
Dangane da fadin masallacin mai alfarma kuwa na harami zai dauki mutane dubu 114 a kowace sa’a domin gudanar da ziyara da ayyukan ibada.
Kuraishi ya ce: dukkanin ayyukan gini a cikin masallaci mai alfarma za su tsaya baki daya a ranar 25 ga watan zul qa’adah, domin bayar da dama ga maniyyata da su shiga cikin haramin mai tsarki domin fara gudanar da ayyukansu na hajjin wannan shekara.
An fara gudanar da aikin gyaran haramin masallacin mai alfarma ne tuna cikin watan Muharram na wanann shekara, domin kara fadinsa ta yadda zai dauki masu ziyara da dama.
3350729