IQNA

An hana Wata Daliba Shiga Ajin Karatu A Kasar Switzerland

23:53 - August 25, 2015
Lambar Labari: 3351569
Bangaren kasa da kasa, an hana wata daliba musulma shiga adomin daukar karatu a wata makaranta sakandare a kasar Switzerland.


Kamfanin dilalncin labaran Iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Le Matin cewa, Arwen Samer daya daga cikin jami’an bangaren ilimi wanna  jaha da abin ya faru ya ce za su gudanar da bincike kan wannan lamari kamar yadda dalibar ta gabatr da koke kan wannan lamari.

Da dama daga cikin jami’an a birnin Ton cikin jahar Bron da ke cikin kasar ta Switzerland sun ce hana dalibai saka hijabi yay i hannun riga da dukaknin kaidoji da kuma dokoki na ilimi a kasar, domin kuwa babu inda aka ce kada wata daliba ta saka hijabin muslunci a cikin ajin karatu.

Wannan mataki dai ya fuskanci akkausar daga bangarori daban-daban na kasar da a kasashen ketare, domin tuna cikin shekara ta 2009 ake saka hijabi a wurin ba tare da wata matasala ba, sai yanzu suka kirkiro hakan.

Wanda hakan yasa ala tilas jami’an makarantar suka kirayi mahaifan wannan yarinya domin tatatunawa da su, da kuma sanin yadda za abullowa lamarin, kuma suna ci gaba da tattaunawa domin warware matsalar.

A shekarar da ta gabata ma an ci zarafin wata karamar yarinya musulma da take saka hijabi yar shekaru 13 a wurin, wanda hakan shi ma ya fuskanci fushin al’umma da dama da kuma kungiyoyin kare hakkin bil adama na yankin.

Musulmin kasar Switzerland sun kai dubu 400 wato kashi 5 cikin dari na dukkanin al’ummar kasar miliyan 8 da suke rayuwa a cikinta.

3351139

Abubuwan Da Ya Shafa: Swis
captcha