IQNA

Za A Gudanar Da Taron Gadir Na Kasa da Kasa Iraki A karo Na 9

23:56 - August 25, 2015
Lambar Labari: 3351572
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da taron gadir na kasa da kasa a Iraki a karo na 9 kamar yadda aka saba gudanarwa a kowace shekara kamar yadda aka sanar.


Kamfanin dilalncin labaran Iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alghadir cewa, a cikin watan Mehr za a gudanar da taron Gadir a mataki na kasa da kasa a Iraki a karo na tara tare da halartar malamai da masana.

Bayanin ya ci gaba da cewa za a gudanar da taron na gadir na kasa da kasa a Iraki ne a karo na 9 kamar yadda aka saba gudanarwa a kowace shekara amma a wanann karon da salon a musamman.

Mutanen kasar Iraki wadanda akasarinsu ambiya tafarkin iyalan gidan amnzon Allah ne suna bayar da muhimamnci ga ranar idin Ghadir da Allah ya umarci amnzonsa domin ayyana wasiyinsa, wanda yam aye gurbinsa.

Bugu da kari kan hakan kasarIraki ta zama nan aka kashe limaman iyalan gidan amnzo da dama suka yi shahada  ahannun azzalumai, da hakan ya hada da shi kansa wasiyin amnzon Allah kuma halifansa a bayansa shugaban muminai.

Yanzu haka dai ana ci gaba da bayyana sunayen mutanen da za su gabatr da jawabai a wajen taron, da suka hada da malamai na cikin gida da kuma wadanda za a gayyata daga kasashen ketare, da suka hada da maamai da kuma masana.

3351288

Abubuwan Da Ya Shafa: iraki
captcha