Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na Ghana Web cewa A cikin watan Nuwamba mai zuwa ne za a bude bankin muslunci a kasar Ghana a hukumance domin gudanar da ayyukansa kamar yadda yake yi a wasu kasashe.
Bayanin ya tababtar da cewa a cikin watan Nuwamban karshen wannans hekara ne bankin musulunci zai fara gudanar da ayyukansa gadan-gadan a kasar Ghana.
Tun a shekarar da ta gabata ce ya kamata bankin ya fara gudanar da ayyukansa a kasar, amma saboda wasu dalilai da suka hada da sharudda na hada-hadar bankuna, hakan ya sanya shirin bude bankin ya kai har wannan shekara.
Bankin musulunci na kasar Ghana zai rika gudanar da harkokinsa bisa ka’idoji na shari’ar muslunci, da hakan ya hada da karbar hannayen jari, bayar da basusuka ba tare da karbar rib aba, kamar yadda zai rika karbar ajiya ba tare da karin rib aba.
Haka nan kuma wanann banki ba zai yi mu’amala da kamfanonin da suke gudanar da ayyuka da suka saba wa shari’ar muslunci ba, kamar kamfanonin giya, ko masu samar da naman alade ko kamfanoni na caca da sauransu, haka nan kuma ba zai saka hannayen jaria irin wadannan kamfanoni ba.
Bankin muslunci a Ghana zai yi mu’amala da musulmi da ma wadanda ba musulmi ba a kan sharuddansa da ka’idojinsa.
3353143