Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Ina cewa, Muhammad Almanyawi shugaban majalisar mabiya addinin muslunci a jahar Monteral da ke kasar Canada ya bukaci da a kafa wata doka amajlaisar dokokin lardin da za ta haramta keta alfarmar addinai.
Wannan bukata ta fuskanci kakakusar suka da martini a majalisar dokokin lardin daga wasu wakilan jam’iyyu masu adawa da musulunc, tare da bayyana hakan da cewa ya saba yancin da jama’a suke da shin a bayyana ra’ayinsu.
Bukatar dai ta hada da hana mutane yin izgili da addinin wasu ko wata akida da takebanci wasu mutane, ko kuma was abubuwa da suke girmamawa masu tsarki a cikin addininsu, domin a girmama ra’ayin kowa da akidarsa.
A bangare guda Nataly Lorwa dan majalisar dokokin kasar Canada ya yi kakakusar suka dangane da wannna bukata da majalisar shawara ta musulmin ta gabatar, inda y ace hakan wani kokari na neman dakile yancin al’ummar kasarsa, kuma hakan ya yi hannun riga da dokokin tsaarin muslkin kasarsu.
3353224