IQNA

An Kame Wani Mutum Mamallakin Wani Wurin Buga Kur’ani A Masar

21:56 - September 07, 2015
Lambar Labari: 3360213
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaron ‘yan sanda sun kame wani mutum da ke mallakar wani wurin buga kur’ani a yankin Daru-salam a birnin Alkahira na Masar saboda buga kur’anin da bai cika ba.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto dagashafin sadarwa na yanar gizo na Veto cewa, Ahmad Muslih mataimakin babban jami’in ‘yan sanda a bangaren bincike  acikin gundumar Daru-salam da ke cikin Alkahira na masar ya bayyana cewa, sun cafke mutumin da ke da wurin, kuma yanzu haka ana gudanar da bincike kan lamarin.

A nasa bangaren bababn jami’in yan sanda na yankiin a bangaren bicike na Daru salam Ahmad Ibrahim ya bayyana cewa, a jiya ne jami’an tsaron ‘yan sanda suka kame mutumin wanda kuma shi ne ke mallakar  wurin buga kur’ani a yankin saboda ya buga wasu kwafi-kwafi na kur’ani da ba su cika ba daidai, saboda an rage shafuka biyu na kur’ani da gangan.

Bayan yaduwa bayanin nasa, tuni jami’an tsaro na cikin kaya suka shiga aikinsu, domin tabbatar da cewa an gano dukkanin adadin kur’anan da ya buga da kuma wadanda suka shiga hannun jama’a gami da wadnda suke a ajiye.

3360103

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha