Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na WAFA cewa, an gudanar da wannan zanga-zanga ne karkashin wani kamfe na nun agoyon baya ga Palastinu.
Kafin wannan lokacin dai fiye da mutane dubu dari ne ne a kasar Birtaniya suka sa hannu, domin neman a kame Firayi ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu idan ya saka kafarsa a cikin kasarsu, domin gurfanar da shi a gaban kotun manyan laifuka ta duniya kan kisan dubban fararen hula a palastinu.
Dubban mutanen sun bukaci da a kame shugaban jam’iyyar ta Likud mai shekaru sittin da biyar da haihuwa a ziyarar da zai kai kasar a ranar Laraba mai zuwa, domin gurfanar da shi a kotun laifukan yaki kan farmakin da ya kai Gaza tsawon kwanaki hamsin a jere yana lugudan wuta kan mata da kanan yara, kuma sa hannun ya kai na mutane dubu dari.
Dukkanin wadanda suka sa hannun sun jadda cewa dole ne a kame Netanyahu saboda kashe fararen hul fiye da dubu biyu a cikin shekarar da ta gabata da ya kaddamar da yaki kan fararen hula a zirin gaza.
Bisa kundin tsarin mulkin kasar bayan da sa hannun ya wuce dubu 10 dole kan gwamnatin Birtaniya ta yi dubi kan lamarin, idan kuma ya kai 100,000 to dole e majalisar dokokin kasar ta zauna akan batun kuma ta sanar da matsayinta a kansa.
KO da yake gqwamnatin Birtaniya ta kare kanta da cewa, jami’an gwamnatoci na kasashen duniya suna da kariya ta siyasa a koina aduniya, saboda haka ba zata aiwatar da abin da ake bukata ba.
A hare-haren da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai Gaza a shekarar 2014 da ta gabata, ta kashe palastinawa 2200, kimanin 577 kuma kanan yara ne, yayin da wasu mutanen fiye da dubu 11 suka samu raunuka.
3360602