Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwatan News cewa, mahukuntan masarautar Saudiyya sun ce an fara guaran wuraren da suka rushe sakamakon faduwar naurar daga kaya, da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 107 tare da jikkatar wasu 238.
Bayanin ya ci gaba da cewa wanmnan hadari yana daga cikin mafi muni da aka taba samu a lokacin gudanar da wannan aiki na ibada, kuma yanzu haka an fara gyaran dukkanin wuraren da abin ya shafa mai fadin mita murabba’I 500 da suka hada warren Safa da Marwa, kuma za a kammala a cikin kankanin lokaci.
Haka nan kuma mahukuntan da masu kula da ayyukan harami sun hana maniyyata hawa zuwa bine na biyu da kuma na uku sakamakon abin da ya faru da kuma gyaran da ake yi.
Wannan na daga cikin manyan naurorin daukar kaya mafi girma guda 10 da suke wurin suna zagaye da harami wadda ta fado kuma ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da jikkatar wasu da suka hada da yan kasar da kuma baki na kasashen waje.
Sabon tsarin ginin haramin dai ana shirin aiwatar da shi ne da zai kai fadin mita murabba’i dubu 400, ta yadda hakan zai bai wa masu aikin ibada miliyan 2 da dubu 200 damar yin aikinsu lokaci guda ba tare da wani cunkoso ba.
3362723