Kamfanin dillancin labaran labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Alwatan ta kasar Saudiyya cewa, Hussain Muhammad Hussain babban daraktan kiwon lafiya na yankin Qasim ya bayyana cewa, sumbantar Hajru Asawa da kuma makam Ibrahim (AS) yana tattare da babban hadari.
Ya ce a halin yanzu babuwa cuta da bulla a kasar ta Saudiyya, amma kuma yin taka tsantsan dangane da sumbantar wurare irin wannan ya zama wajibi, domin kare kai daga kamuwa daga cutuka.
Wannan jami’I ya bayyan hakan ne bisa fakewa da dalilai na lafiya domin aiwatar da abin malaman wahabiya suka yi Imani da shi, na cewa wadannan wurare ba su da wata alfarma da za a mayar da hankalia kanta, kuma suna cewa neman tabarruki a wannan wuri bidi’a ne.
Malaman wahabiyawan Saudiyya sun jima sun yada irin wannan mummunan tunani ta yadda ya kai a halin yanzu ana rusa wurare masu alfarma na tarihin muslnci da sunan ana fadada dakin Ka’abah da masallacin manzo.
3363009