Kamfanin dilalncin labaran Alshabiba cewa Ahamd Muhamamd Alhassan matashi dan shekaru 14 da haihuwa yak era wata agogon hannu a jahar Dalas ta kasar Amurka, wanda hakan ya sanya malaman makarantarsu suka ci zarafinsa tare da bayyana cewa ya saka bam a cikinta.
Wanann lamari ya sanya shugaban kasar Amurka ya gayyace shi zuwa fadar white house domin nuna goyon bayansa ga yaron da kuma tausaya masa, gami da kara bashi karfin gwiwa kan kokarin da ya yi domin kada a kashe masa zuciya.
Shugaban na Amurka y ace muna son wannan yaro Ahmad Muhamamd Alhassan ya zo da agogonsa zuwa wannan fada domin nuna ta amatsayin wani gagarumin aiki da wani matashi ya yi a kasar kuma hakan ya zama a bin koyi ga sauran matasa.
Wannan lamari ya fuskanci kakakusar suka daga wasu yan siyasa kan gayyatar da Obama yay i wa wannan matashi, kamar yadda su ma bangaren tsaron fadar shugaban na Amurka sun nuna damuwa kan kan hakan, tare da danagnata hakan da batun tsaro.
Wasu masu tsananin kiyayya da musulunci da musulmi a Amurka sun yi ta yadawa a shafin yanar gizo na cewa yarin yana da alaka da yan ta’adda kuma karbar a fadar shugaban kasa daure ma ta’addanci gindi ne.
Yayin da kuma kungoyn musulmi da na kare hakkin bil adama a Amurka a shafin sadarwa na IStandWithAhmed sun yi ta sukar lamirin gwamnati kan cin zarafin yaron, wanda ake ganin hakan ne ya sanya Obama daukar wannan mataki.
3364576