Kamfanin dillancin labaran Iqna ya ahbarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-alam cewa, Sayyid Hassan Nasrullaha tattaunawarsa da Almanar ya bayyana cewa matsalolin da aka samu a Hajjin bana yan ada alaka da sakacin masu shirya aikin kamar yadda ya kamata.
Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon Sayyid Hasan Nasrullahi ya jaddada cewa ya zame dole a kan mahukuntan Saudiyya su mika ragamar jagorancin gudanar da ayyukan hajji ga kasashen musulmi.
A ganawarsa da tashar a jiya Juma’a: Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi da ke kasar Lebanon Sayyid Hasan Nasrullahi ya bayyana cewar sakamakon gazawar mahukuntan Saudiyya a fagen iya gudanar da jagorancin ayyukan hajji, ya zame dole su amince da shawarar mika ragamar tsara gudanar da ayyukan hajji a hannun kwamitin kasashen musulmi.
Har ila yau Sayyid Hasan Nasrullahi ya daura alhakin hatsarin da ya faru a Minna a ranar sallah kan mahukuntan Saudiyya saboda sune hakkin kula da lafiyar mahajjata ya hau kansu.
Abin da ya faruwar daruruwan alahazai yana ci gaba da fuskantar kakkausar suka daga bangarori na kasashen duniya, tare da yin kira da akwace wannan aiki daga masarautar mulkin mulukiya, tare da mayar da lamarin ga kasashen musulmi.
Har yanzu hukumomin Saudiyya ba su bayani a hukumance ba kan adaddin mutanen da suka rasu da kuma kasashensu, yayin da wasu daga cikin kasashen duniya suka fara sanar da adadin alhazansu da suka rasa rayukansu ko suka bata a turereniyar da ta wakana a Mina.
Bisa irin bayanan da suke fitowa daga Saudiyya, alhazan kasar Iran ne suka fi mutuwa da kuma salwanta a wannan mummunan hadari na Mina, yayin da wasu rahotanni ke cewa daga cikin wadanda suka rasu har da jami’an diplomasiyyah shida na kasar.