Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almisriyun cewa, wasu kafofin yada labarai daga kasar Saudiyya sun ce mahukuntan kasar sun fara rufe mutane tun jiya a wasu manyan kabruka kimanin mutane 600 da ba a san ko suwane ne ba.
Hukumomin na Saudiyya dai suna ta bode adadinin mutanen mutanen da suka rasa rayukansu saboda wasu dalilai da ba asani ba, amma wasu majiyoyin na gefe da suka samo bayanin abin da ke faruwa suna bayar da bayanai.
Yanzu haka dai an tabbatar da cewa kimanin mutane dubu hudu suka rasa rayukansu sakamakon abin da ya faru a wajen aikin hajji na bana, duk kwa da cewa har yanzu ana ci gaba da gane wasu wadanda ba tantance sub a.
Muhammad Mukhtar Juma’a shi ne minister mai kula da harkokin addini akasar Masar ya bayyana cewa, ya uwa sun iya tantance gawawwakin mutanen kasarsu kamar 37, yayin da kuma wasu suka bata, ana ci gab ada bincike kan lamarinsu.
3374142