IQNA

Masallatan Chicago Suna Karbar Bakuncin Wadanda Ba Musulmi Ba

22:57 - October 04, 2015
Lambar Labari: 3379496
Bangaren kasa da kasa, masallatan birnin Chicago na kasar Amurka suna karbar bakuncin wasu daga cikin mutanen birnin wadanda ba musulmi ba domin bayyana musu abin da suke bukatar sani daga muslunci.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Daily Herald cewa, Tabassum Halim shugaban kwamitin musulmi mai suna Greater Chicago ya bayyana cewa, suna gudanar da irin wannan taro bayan lokaci zuwa lokaci.

Ya ci gaba da cewa akwai mutane da dama da suke da rashin masaniya dangane da addinin muslunci daga cikin Amurkawa, kuma babu wanda zai ba su bayanin da suke bukata da kuma tambayoyin da suke da su dangane da addini.

Tabassum ya ce sukan gudanar da irin wannan taro kuma Amurkawa da dama suna halartarsa suna gabatar da abubwan da ske bukatar sani kan addini, kuma ana ba su amsa gwargwadon iko, kuma ana samun sara kan hakan.

Wasu daga cikin masu tsananin kiyayya da muslunci suna yin amfani da damar da suke da ita a wanann lokacin da wasu suke kaddamar da ayyukan ta’addanci da sunan muslunci, inda suke bayyana hakan a matsayin shi ne koyarwar muslunci.

Ana bayar da kayan abinci da da nasha gab akin da ska halartar tare da nuna musu dabiu irin wadanda muslnci ya koyar da dana dam.

A lokutan salla kuma sukan bar muslmi daga cikin mahaarta wurin domin su gudanar da salla kafin daga bisani bayan kammalawa  aci gabab da taron da ake yi.

3379099

Abubuwan Da Ya Shafa: amurka
captcha