IQNA

An Fara Gudanar Da Taron Kur’ani Da Sunna Karo Na Takwas A Kasar Masar

23:21 - October 05, 2015
Lambar Labari: 3382032
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani zaman taro kara wa juna sani mai taken kurani da sunan karo na takwas a kasar masar a jami’ar Mansurah.


Kamfanin dilalncin labaran iqnan ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz na Alfajr cewa, Muhammad Alqannawi shugaban jami’ar Almansurah ne ya jagoranci bude wanann aman taro.

Wannan taro an kwashe shekaru takwas a jere ana gudanar da shia  akasar ta Masar, wanda wannan karon ya dauki taken kur’ani da sunna ta mahangar ilimi.

Muhammad Alqannawi da Abdullah Musleh shugaban cibiyar gahiyarwar kur’ani mai tsarki ta duniya su ne suka dauki nauyin shirya taron.

Mustafa a Alshaimi wanda shi ma ammba ne wannan kungiya ya bayyana a cikin wani jawabi da ya gabatar a wurin cewa, dukkanin abin da ake gudanarwa ya dace ya zama bisa mahanga ta ilimi.

Ya ce muna rayuwa a wani zamani da ilimin kur’ani da sunan suke kusa da mutane a kowane lokaci a cikin harkokinsu, inda ya buga misali da surar farko ta kur’ani wadda ta fara da Qalam, ma’ana daga ilimi wato karatu da rubutu, tare da yin ishara da hadisai na ilimi 1800 a ciki.

Hussain Hamdan wanda shi ma malami ne a jami’ar ta Almansurah ya bayyana a cikin wani jawabi da ya gabatar a wurin cewa, tun kafin turawa su san wani abu kan ilimi muslunci ya sanar da musulmi ilimi.

A nasa bangaren shugaban jami’ar ta Almansurah ya jaddad wajabcin karfa dukaknin bangarori na biinciken ilimi a tsakanin musulmi domin su zama cikin masani kan dukaknin bangarori.

Wannan taron dai yana yin dubi ne kan bangarori 13 na ilimi kamar dai yadda masu shirya taron suka sanar, wanda kuma akansu ne ake tatatunawa.

3381630

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha