Kamfanin dilalncin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Tena cewa, a yau Hamas ta kirayi dukaknin palastinawa da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin yin jerin gwano da nuna rashin amincewa da keta alfarmar wurare masu tsarki.
Tun Dai bayan cimam yarjjeniyar sulhu tsakanin palastinawa da Isra’ila babu ko daya daga cikin abubuwan da yarjejeniyar ta kunsa da aka aiwatar, da hakn ya hada da batun kafa kasar Palastinu mai cin gishin kanta daga Gaza har zuwa Ariha.
Da kuma baiwa miliyoyin palastinawa da Isra’ila ta kora suke gudun hijira a kasashen larabawa damar komawa gidajensu, da sauran batutuwa wadanad asuka shafi hakkokin palastinawa da Isra’ila ta take da yarjejeniyar ta amince a mayar musu.
A wannan karon Palastinawan sun fara wani sabon bore tare da yin amfani da salon daba wuka kan yahudawan sahyuniya da ke zaluntarsu, wanda kuma yake fadada a tsakanin palastinawa.
Wanda kuma shi ne bore da yafi daga hankalin Isra’ila da yahudawa atsakanin dukkanin irin boren da palastinawa suka yi na tsawon shekaru, wanda kuma yake samun amincewar dukkanin kungiyoyin palastiwa har ma da wadanda ba na gwagwarmaya ba.
3385804