IQNA

Wata Kirista bYa tarjama Kur’ani Mai Tsarki Da Harshen Kurame

23:20 - October 19, 2015
Lambar Labari: 3390454
Bangaren kasa da kasa, Najla Ta’at Ghali mabiya addinain kiristanci ce wadda ta tarjama kur’ani mai tsarki baki daya a cikin harshen ishara da kurame suke magana da shi a garin Bani Yusuf na kasar Masar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-watan cewa, Najla Ta’at Ghali wata mat ace kirista wadda ta tarjama kur’ani mai tsarki a cikin harshen ishara da kurame suke magana da shi yaka junansu.

Ta ce ita aikinta shi ne tarjama, kuma duk abin da aka bata za ta tarjama shi domin amfanin marassa magan wato kurame, kuma ba ta ga wani dalili da zai hana ta tarjama kur’ani ba domin kurame su fahimci ma’anoninsa.

Wannan mata kirista ta ce saboda ta samu natsuwa da cewa tarjama kur’ani bai saba wa shari bas hi yasa ta tarjama shi ga kurame, kuma tana ganin hakan a matsayin wani mai matukar amfani.

Ta kara da cewa kafin ta fara gudanar da wannan aiki sai ta ta tambayi wasu daga manyan malamai na musulmi a kan cewa ko wannan aiki yana da matsala ta fuskar shari’a amma sun amsa mata da cewa babu wata matsala a shar’ance.

3388488

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha